Dani Alves zai shafe makwanni biyu yana jinya

alves
Image caption Dani Alves

Dan kwallon Brazil wanda ke bugawa Barcelona kwallo Dani Alves zai shafe akalla makwanni biyu yana jinyar rauni a kafarshi.

Alves ya jimu ne a wasansu da Malaga inda aka fitar dashi minti ashirin da hudu da fara wasan.

Likitoci a Nou Camp sunyi gwaje gwaje akan Alves kuma sun gano matsala a kafarshi ta dama abinda ya sa dole ne sai ya murmure zai koma fagen fama.

Dalilin wannan jinyar, Alves ba zai buga wasan Barca da Racing Santander da kuma na Hercules da kuma bugu na biyu na kofin Fa tsakaninsu Betis.