An ci tarar Babel saboda kalamanshi a Twitter

babel
Image caption Ryan Babel

An ci tarar dan kwallon Liverpool Ryan Babel pan dubu goma saboda kalaman daya rubuta a shafin sadarwa ta Twitter,sannan an gargadeshi kada ya sake.

Dan kwallon Holland din ya nuna hoton akalin wasa Howard Webb sanye da rigar Manchester United bayanda Liverpool ta sha kashi a Old Trafford daci daya me ban haushi.

Babel ya amsa laifin aikata ba dai dai ba a lokacin daya gurfana gaban hukumar kula da bin ka'idoji na hukumar kwallon kafa ta Ingila.

Shugaban hukumar Roger Burden ya ce"shafin sadarwa kamar Twitter ana daukarshi tamkar magana ce a bainar jama'a".

Daga bayan Babel ya nemi afuwa amma hakan bai sa an fasa ladabtar dashi ba.