Darren Bent ya mikawa Sunderland takarda

bent
Image caption Darren Bent

Kungiyar Sunderland ta tabbatar cewa Darren Bent ya bada a rubuce yanason ya barsu a daidai lokacin da Aston Villa ke zawarcin dan kwallon.

Rahotanni sun nuna cewar Villa na shirin bada pan miliyan goma sha takwas akan dan kwallon Ingila.

Bent me shekaru 26 ya koma Sunderland ne daga Tottenham akan pam miliyan goma a watan Agustan 2009 a yarjejeniya ta shekaru hudu.

Bent ya zira kwallaye 25 a kakar wasan data wuce a halin yanzu kuma ya zira kwallaye 11 a kakar wasa ta bana.

Takwas daga cikin kwallayen ya zira su a gasar premier inda ya taimakawa Sunderland take ta shida akan tebur.

Koda yake dai ba'a gayyaci Bent cikin tawagar Ingila a gasar cin kofin duniya ba, amma ya zira kwallo a wasanshi na farko daya buga mata a watan Satumba a tsakanin Ingila da Switzerland.