La Liga:Dole sai mun zage damtse-Mourinho

mourinho
Image caption Mourinho gwarzon kocin duniya

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce dole sai kungiyarshi ta zage damtse idan har tanason kwace kofin gasar La liga daga hannun Barcelona.

Real ta fara kakar wasan bana da karfinta karkashin kocin dan asalin Portugal inda ta lashe wasanni 15 cikin 18.

Amma a halin yanzu Barcelona ta dara ta da maki hudu sakamakon kunen dokin da Real ta tashi tsakaninta da Almeriya a ranar Lahadi, abinda yasa Mourinho ya ce ba zasu kara bari a dokesu ko su tashi canjaras ba.

Mourinho yace "tashi canjaras kamar rasa maki biyu ne".

Mourinho ya nuna rashin gamsuwarshi akan hukuncin da alkalin wasa ya dauka na kin bada penariti akan yarda Karim Benzema da Cristiano Ronaldo, sannan kuma da rike kwallo da hannun da Modeste M'Bami yayi ba tare da an hukunta shi ba.