Shola Ameobi na murnar kiran da Najeriya tayi mashi

ameobi
Image caption Shola Ameobi

Dan kwallon Newcastle United Shola Ameobi ya ce yana murnar sake samun damar bugawa Najeriya kwallo a karon farko matakin Super Eagles.

Ameobi me shekaru 29, ya bugawa Ingila kwallo a matakin 'yan kasada shekaru 21 kuma an gayyaceshi ya buga a wasan sada zumunci tsakanin Najeriya da Guatemala a wata mai zuwa.

Haka zalika dan kwallon Wigan Athletic Victor Moses shima yana cikin wadanda aka gayyata a tawagar.

Kocin Super Eagles Samson Siasia ya ce Moses ya nuna farin cikin samun wannan damar amma dai kulob dinshi ya shaidawa BBC cewar bai sanarda ita ba akan gayyatar.

An haifi Ameobi ne a Zaria dake jihar Kaduna kafin ya koma Ingila tare da iyayenshi yana dan shekara biyar kuma shekaru goma da suka wuce an gayyaceshi ya bugawa Najeriya amma sai yaki yarda.