Pienaar yafi son Tottenham akan Chelsea

pienaar
Image caption Steven Pienaar

Dan kwallon Everton Steven Pienaar ya bayyana cewar zai koma Tottenham bayanda kungiyoyin biyu suka amince pan miliyan biyu da rabi.

Dan kwallon mai shekaru 28 ya ziyarci filin horon Spurs a ranar Talata kuma ana saran zai kulla yarjejeniya ta shekaru hudu da kungiyar bayan an gwada lafiyarshi.

Domin kawo karshen jita jita sai dan kwallon Afrika ta Kudu Pienaar ya rubuta a Twitter cewar" zan tafi Spurs".

Chelsea tayi zawarcin dan kwallon daga Everton,amma ta kasa shawo kan dan kwallon ya rabatta hannu a yarjejeniya da ita.

Koda yake Tottenham ko Everton basu tabbatar da yarjejeniyar ba,amma Pienaar ya kara da cewar: "naji dadin zama na a Everton kuma ba zan taba mantawa da ita ba".