Real Madrid na bukatar sabon dan kwallo-Ronaldo

ronaldo
Image caption Christiano Ronaldo

Dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce dole ne sai an siyo sabon dan kwallon gaba don kwace kofin gasar La Liga daga wajen Barcelona.

Ronaldo yace"muna bukatar sabon dan kwallo na watanni shida".

Real a halin yanzu na karancin 'yan kwallon gaba saboda Gonzalo Higuain dan Argentina an yi mashi tiyata a Amurka abinda zai hanashi taka leda na kusan watanni hudu.

Ronaldo yace idan har ana bukatar samun nasarori dole ne sai an samu 'yan kwallo kuma na ji dadin cewar ana tuntubar van Nistelrooy.

Real Madrid a yanzu Barcelona tafi ta da maki hudu kuma Barca nada zaratan 'yan kwallon biyu a gabanta wato Lionel Messi da David Villa wadanda a duk wasa dole sai dayansu ya zira kwallo.