Martin O'Neill ba zai je West Ham ba

Martin O'Neill
Image caption Bai ji dadin yadda aka tsaigunta bayanan komawarsa West Ham din ga kafafen yada labarai ba

Wasu bayanai da BBC ta samu sun nuna cewa Martin O'Neill ya cire kansa daga cikin masu neman mukamin kocin West Ham.

An sa ran tsohon kocin na Aston Villa zai maye gurbin Avram Grant a Upton Park a wannan makon.

Amma wakilin BBC Pat Murphy ya ce: "A yadda nake kallon abin zai yi wuya ya karbi wannan aikin.

"Martin O'Neill ba ya sahun kocin da suke gaggawa wajen daukar mataki. Yana taka tsantsan kafin ya daukar mataki na gaba a kan rayuwarsa".

An kuma bayyana cewa kocin bai ji dadin yadda aka tsaigunta bayanan komawarsa West Ham din ga kafafen yada labarai ba, a daidai lokacin kungiyar ke shirin taka leda da Arsenal.