An nada Eric Cantona darektan kungiyar Cosmos

cantona
Image caption Eric Cantona

An nada tsohon dan kwallon Manchester United Eric Cantona a matsayin darektan kulob din New York Cosmos na Amurka.

Cantona mai shekaru 44 wanda yayi ritaya daga kwallo a shekarar 1997 ya ce"wannan shirin na musamman ne kuma hada ke tsakanin kwallon kafa da aiki".

Kungiyar Cosmos wacce a baya take tare da dan kwallon Brazil Pele, a shekarar 1985 ta rushe amma sai a watan Agustan bara tsohon darektan Tottenham Paul Kelmsey ya kara kaddamar da ita.

Sabuwar kulob din Cantona a halin yanzu baida 'yan kwallo ko filin wasa amma yana saran zai buga gasa daban daban.

A sanarwar nadin da aka yiwa Cantona, Cosmos ta c dan Faransa zai samar da shugabanci na nagari don bunkasa 'yan kwallo.