Anichebe ya sabunta kwangilarshi a Everton

anichebe
Image caption Victor Anichebe

'Yan kwallon Everton Victor Anichebe da Seamus Coleman duk sun sabunta yarjejeniyarsu na karin hudu da rabi masu zuwa.

Dan kwallon Najeriya Anichebe mai shekaru 22 a kwannan ya murmure daga ciwon gwiwa.

Shima dai Coleman wanda ya zira kwallaye biyar a kakar wasa ta bana, ya kasance daya daga cikin 'yan kwallon dake haskakawa.

Sabunta kwangilar da Anichebe yayi , ya kawo karshen jita jitar raba gari da kungiyar idan kwangilarshi ta kare a karshen kakar wasa ta bana.

Coleman dan Jamhuriyar Ireland ya kula yarjejeniyar farko ne da Everton a watan Mayun bara.