Arsenal ta doke Leeds a gasar FA

Arsenal ta doke Leeds a gasar FA
Image caption A yanzu Arsenal za ta kara ne da Huddersfield Town na League One

Arsenal ta doke Leeds da ci 3-1 a zagaye na uku na gasar cin kofin FA, inda ta samu damar tsallake wa zuwa zagaye na hudu.

Arsenal ta mamaye wasan tun daga farko har zuwa karshe, inda Samir Nasri ya zira kwallon farko.

Bacary Sagna ne ya zira kwallo ta biyu, kafin Bradley Johnson ya zira wa Leeds kwallo dayan da ta samu.

Dan wasan Holan Robin van Persie ne ya zira kwallo ta uku bayan da Nicklas Bendtner ya taimaka masa.

Arsenal, wacce ke da damar lashe kofuna hudu a kakar bana, a yanzu za ta kara ne da Huddersfield Town na League One.