Dan Ghana Ibrahim Ayew ya bar Zamalek ya koma Belgium

ayew
Image caption Ibrahim Ayew ya bar Zamalek

Dan kwallon Ghana Ibrahim Ayew ya koma Belgium inda ya kulla yarjejeniya da kungiyar Lierse.

Dan shekaru 22 da haihuwa, Ayew ya amince da kwangila ta shekaru biyu abinda kuma ya kawo karshen zamansa a kungiyar Zamalek ta Masar.

Kakakin Lierse ya shaidawa BBC cewar "zan iya tabbatar da cewa Ibrahim Ayew ya shiga cikin tawagarmu".

Ana saran Ayew zai buga wasan farko a Lierse a mako mai zuwa inda zasu kara Charleroi a gasar kwallon Belgium.

Dan kwallon dai na cikin tawagar Black Stars a Afrika ta Kudu lokacin gasar cin kofin duniya a bara, kuma ya zaku ya bar Zamalek saboda baya samun damar bugawa.

Ayew, shine babban dan Abedi Ayew 'pele' wato shahararren dan kwallon Ghana dinan.