Tennis: Nadal ya lallasa Ryan Sweeting

Rafael Nadal
Image caption Wannan gasar ta Australian Open ita ce ta farko a kakar bana

Rafael Nadal na ci gaba da haskaka wa a gasar Australian Open bayan da ya lallasa Ryan Sweeting da ci 6-2 6-1 6-1 a zagaye na biyu.

Nadal, wanda ya lashe gasar a shekara ta 2009, ya lashe zagayen farko ne a cikin mintina 28, kafin ya fadi wasa guda a minti na 38.

Sweeting dan kasar Amurka ya dan farfado a zagaye na uku, amma duk da haka Nadal ya yi kaca-kaca da shi.

Michael Llodra, wanda ke mataki na 22 a duniya, ya sha kashi a hannun Milos Raonic da ci 7-6 (7-3) 6-3 7-6 (7-4).