CAN U 17: Burkina Faso ta doke Rwanda a wasan karshe

Burkina Faso
Image caption Wannan ne karon farko da Burkina Faso ta samu nasara a kwallon matasa

Burkina Faso ta lashe gasar cin kofin matasan Afrika 'yan kasada shekaru 17 bayan ta samu galaba akan Rwanda mai masaukin baki daci biyu da daya a wasan karshe.

Zaniou Sana ne fara zira a ragar Rwanda kafin Tibingana Mwesigye ya farke.

Amma sai matasan Burkina Fason suka yi kukan kura inda Kabore Abdoul Aziz ya ci kwallon daya basu nasara.

A lokacin wasan dai an kori dan kwallon Burkina Kanazoe Bassirou ana sauran minti talatin a tashi wasan.

Burkina Faso a baya sau biyu ta buga wasan karshe na gasar cin kofin matasan Afrika 'yan kasada shekaru 17, inda Ghana ta doke ta a shekarar 1999 sai Najeriya ta samu galaba akanta a shekara ta 200.

Ita kuwa Rwanda wannan ne karon farko data buga wasan karshe na gasar.