Demba Ba zai koma West Ham

Demba Ba zai koma West Ham
Image caption West Ham ta dade tana neman Demba Ba

Dan wasan Hoffenheim Demba Ba na gab da kulla yarjejeniyar wucin gadi da West Ham kamar yadda shugaban kulob din Ernst Tanner ya bayyana.

"Ba a sa hannu kan wata yarjejeniya ba, amma kusan komai ya kankama a game da komawarsa West Ham," kamar yadda ya ce.

Dan wasan na Senegal ya samu rashin jituwa da Hoffenheim ne a farkon watan nan bayan da ya ki amince wa ya yi horo.

Yunkurin da dan wasan ya yi a baya na koma wa Stoke a kan fan miliyan 6 ya ci tura bayan da ya fadi a gwajin lafiyar da ya yi.

Sai dai ya yi gwajin lafiyar ba tare da matsala ba a West Ham, kuma ana saran za a kammala batun nan ba da jimawa.