Chelsea ta lallasa Bolton da ci 4-0

Chelsea ta lallasa Bolton da ci 4-0
Image caption Wannan nasara ta kara wa Chelsea kwarin gwiwa

Yunkurin Chelsea na lashe gasar Premier ya farfado bayan da su ka lallasa Bolton da ci 4-0 a filin wasa na Reebok.

Didier Drogba ne ya fara zira kwallon farko jim kadan da fara wasan.

Matt Taylor ya so ya rama wa Bolton amma sai Petr Cech ya hana shi, kafin daga bisani Florent Malouda ya zira wa Chelsea kwallo ta biyu.

Nicolas Anelka ne ya zira kwallo ta uku kafin Ramires ya zira ta hudu.

Wannan nasara ta nuna cewa shekaru 13 kenan Bolton ta shafe ba ta yi nasara a kan Chelsea ba a filin Reebok.

Kuma ta nuna yadda Chelsea ke farfado wa bayan da ta samu koma baya a 'yan makwannin da su ka gabata.