NFF:Lulu ya janye kara akan shugabancin Maigari

lulu
Image caption An tsige Sani Lulu akan zargin cin hanci da rashawa

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa a Najeriya NFF Alhaji Sani Lulu wanda aka tsige ya janye karar daya shigar gaban kotun sasanta batutuwan wasanni ta duniya wato CAS dake Switzerland.

Lulu da tsohon mataimakinshi Amanze Uchegbulam da Taiwo Ogunjobi sun kai karar NFF ne akan cewar an saba ka'ida wajen tsigesu daga kan mukamansu a bara.

Lauyan dake wakiltar mutannen uku A.P Ameh ya ce shawarar janye karar nada nufin shawokan matsalar ta wata hanyar.

A cewar Ameh"shiga tsakani da shugaban Caf Isa Hayatou yayi shine abinda yasa muka janye karar".

Wasikar da aka rubutawa CAS ta ce "soke haramtaccen tsigewar da aka yiwa jami'an NFF a ranar 28 ga watan Disamba da kuma nada sabon ministan wasanni ya nuna cewar akwai alamun sake fasali don bunkasa wasanni".

A bara ne bayan Super Eagles ta taka mummunar rawa a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu, aka tsige Sani Lulu, da Uchegbulam da Ogunjobi bisa zargin cin hanci da rashawa.