Tennis: Andy Murray ya lallasa Jurgen Melzer

Andy Murray
Image caption Andy Murray ne na daya a wasan Tennis a Burtaniya

Dan Burtaniya Andy Murray ya lallasa Jurgen Melzer a gasar Australian Open da ci 6-3 6-1 6-1, inda a yanzu ya kai zagayen dab da na kusa da karshe.

Murry wanda shi ne na biyar a tsarin gasar ya nuna bajinta sosai kan abokin karawar ta sa dan kasar Austria.

Murry dan shekaru 23, ya lashe wasan ne a mintina 103.

A yanzu dan wasan, wanda ya fito daga yankin Scotland zai fafata ne da Alexandr Dolgopolov wanda ya doke Robin Soderling.

"Na ji dadi sosai, saboda wasa ne da na yi tsammanin zai wahalar da ni, amma sai na samu nasara," a cewar Murry.