Arsenal na zawarcin Oxlade-Chamberlain daga Southampton

wenger
Image caption Wenger ya kware wajen zakulo matasa

Kocin Arsenal Arsene Wenger yace yana saran zai kulla yarjejeniya da dan kwallon Southampton Alex Oxlade-Chamberlain.

Dan kwallon mai shekaru goma sha bakwai wasu kungiyoyi kamarsu Liverpool, Tottenham da Fulham suna zawarcinshi, amma dai Wenger ya nuna kwadayin samun galaba akan abokan hamayyarshi.

Wenger yace "muna bukatar yarjejeniya da dan kwallon kuma muna matsa lamba don mu cimma bukatarmu".

A cewar Wenger, Oxlade-Chamberlain zai zo Arsenal saboda yadda kungiyar ke rainon matasa kamar yadda tayi wa 'yan kwallon kamarsu Cesc Fabregas da Theo Walcott da Jack Wilshire.