Adebayor ya koma Real Madrid daga Manchester City

adebayor
Image caption Emmanuel Adebayor na takun saka da Mancini

Dan kwallon Manchester City Emmanuel Adebayor ya koma Real Madrid na wucin gadi har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Ana saran Adebayor a ranar Laraba zai tafi Spain don a gwada lafiyarshi.

Madrid nada damar sayen dan kwallon mai shekaru ashirin da shida bayan karewar kwangilar.

Adebayor ya koma Manchester City daga Arsenal akan pan miliyan 25 a shekera ta 2009 inda ya zira kwallaye 19 cikin wasanni 36 .

A kwanan kocin City Roberto Mancini na takun saka da Adebayor saboda baya samun damar buga kwallo.