An zabi David Bernstein a matsayin shugaban hukumar kwallon Ingila

bernstein
Image caption David Bernstein

An zabi tsohon shugaban Manchester City David Bernstein a matsayin shugaban hukumar dake kula da kwallon kafa a Ingila wato FA.

Bernstein me shekaru 67 a watan Disamban bara ne kwamitin gudunarwar hukumar da gagarumin rinjaye ya amince da bashi mukamin sannan kuma sai majalisar kwallon kafar itama ta rabbata hannu akan zaben.

Mataimakin kungiyar Arsenal David Dein ne aka yita hasashen zai sami mukamin bayanda Lord Triesman yayi murabus a watan Mayun bara.

Amma sai aka mika sunan Bernstein bayanda wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban Bolton Phil Gartside ya bada sunanshi.