Van Bommel ya bar Bayern ya koma AC Milan

bommel
Image caption Mark van Bommel

Kaptin din Bayern Munich Mark van Bommel ya koma AC Milan watanni biyar kafin kwangilarshi ta kare.

Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce "burin Mark ne ya koma Ac Milan ba tare bata lokaci ba kafin kwangilarshi ta kare".

Bayern bata bada bayanai ba akan kudin da aka kashe na cinikin amma dai rahotanni sun nuna cewar van Bommel yana takun saka da kocinsa Louis van Gaal.

Van Bommel ya koma Bayern ne a shekara ta 2006 akan Euro miliyan shida daga Barcelona,kuma ya buga wasanni 123 inda ya zira kwallaye 11 a Jamus din.

Dan kwallon Holland din mai shekaru talatin da uku yace"zan bar Bayern Munich cikin damuwa tare da bugun kirjin nayi abin azo a gani".