Chelsea ta karyata batun zawarcin Aguero na Athletico

aguero
Image caption Sergio Aguero

Chelsea ta karyata cewa bata bada tayin pan miliyan hamsin da biyu ba akan 'yan kwallon Atletico Madrid Sergio Aguero da Diego Godin.

Atletico ta bayyana cewar kulob biyu sun nuna sha'awarsu akan 'yan kwallonta daya daga Chelsea da kuma pan miliyan talatin da tara daga Real Madrid akan Aguero.

Chelsea dai taki cewa komai akan wanan jita jitar.

Amma dai BBC ta fahimci cewar zakarun kwallon premier din basu ji dadin wannan rahoton daya fito daga Spain ba.

Aguero dan Argentina mai shekaru 22 ya zira kwallaye bakwai a kakar wasa ta bana.