Dan Chelsea Kakuta ya koma Fulham

kakuta
Image caption Gael Kakuta

Dan kwallon Chelsea Gael Kakuta ya koma Fulham na wucin gadi har zuwa karshen kakar wasan bana.

Dan wasan mai shekaru goma sha tara an gwada lafiyarshi a Fulham, amma ba zai buga wasanta da Liverpool ba na ranar Laraba.

Akwai shakku akan cewar Kakuta ba zai buga wasan Fulham da Tottenham na ranar Lahadi a gasar cin kofin FA.

Shima wani matashin dan kwallon Chelsea Patrick van Aanholt, ya koma Leicester a matsayin aro.

Dan Holland din mai shekaru 20, ya koma Chelsea daga PSV Eindhoven a shekara ta 2007.