Sunderland na zawarcin Sulley Muntari daga Inter

muntari
Image caption Sulley Muntari

An baiwa Sunderland damar tattaunawa don kulla yarjejeniya da dan kwallon Inter Milan Sulley Muntari.

Idan har suka sasanta, dan kwallon mai shekaru ashirin da shida zai koma Black Cats har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

A baya Muntari ya taka leda a gasar Premier League tare da Portsmouth a shekara ta 2007-08 kafin ya koma Inter.

Muntari ya lashe gasar serie A da Inter sau biyu a jere da kuma gasar zakarun Turai a shekara ta 2010.

Idan har ya koma Sunderland zai hade da 'yan uwanshi 'yan Ghana Asamoah Gyan da John Mensah.