Babu tabbas ko can cigaba da tamaula har badi-Scholes

scholes
Image caption Scholes da Giggs sun dade suna taka leda

Dan kwallon Manchester United Paul Scholes ya ce babu tabbas ko zai cigaba da taka leda har zuwa badi.

Scholes da Ryan Giggs sun riga sun ce zasu sanya hannun a sabuwar yarjejeniya a Old Trafford duk da cewar Scholes din ya kai shekaru 37.

A kwannan ne Scholes ya murmure daga jinya mai tsawo da yayi abinda wasu ke ganin ba zai bari ya takura kanshi ba.

Scholes ya shaidawa MUTV cewar "ban san abinda zanyi a badi ba".

Ya kara da cewar zan maida hankali ne wajen murmurewa daga raunin daya dade yana damu na.