Busquets ya sabunta kwangilarshi da Barca zuwa 2015.

busquets
Image caption Mahaifin Sergio Busquets tsohon dan kwallon Barca ne

Dan kwallon Barcelona Sergio Busquets ya sabunta yarjejeniyarshi da ita har zuwa shekara ta 2015.

Wannan yarjejeniyar da dan kwallon mai shekaru ashirin da biyu ya sabunta ta kara yawan kudaden da ake bashi daga euro miliyan tamanin zuwa euro miliyan dari da hamsin.

Busquets ya shaidawa tashar talabijin na Barca cewar "na yi murna kuma haka ne yadda ya kamata ya bude sabuwar shekara, labari ne me dadi ga kowa".

Busquets ya fara bugawa babbar tawagar Barca ne a shekara ta 2008 karkashin jagorancin Josep Guardiola kuma a baya kwangilarshi ya kamata ta kare ne a shekara ta 2013.

Mahaifin Busquets mai suna Carles tsohon golan Barcelona ne kuma dashi a lashe gasar zakarun Turai a shekarar 1992,abinda ke nufin cewar daa da uba sun lashe wannan gasar tunda Busquets ya lashe a 2009.