Tennis: Novak Djokovic ya fidda Roger Federer

djokivic
Image caption Novak Djokovic

Novak Djokovic na kan hanyar sake lashe babban kofi na gasar tennis bayan da yakai wasan karshe sakamakon fidda Roger Federer a zagayen kusada karshe na gasar Australian open.

Djokovic dan kasar Serbia ya samu galaba akan Federer ne da seti uku da daya wato 7-6 (7-3) 7-5 6-4.

Djokovic zai hadu da wanda ya samu nasara a tsakanin Andy Murray da David Ferrer a karawar da zasu yi a ranar Juma'a.

A bangaren mata Li Na ta kasance 'yar kasar China ta farko da zata buga wasan karshe na babban gasa a tennis, bayan da Li Na din ta doke Caroline Wozniaki.

Li Na zata fafata da Kim Clijsters a wasan karshe a ranar Asabar.