Ameobi zai buga a wasan Najeriya da Guatemala-Siasia

ameobi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shola Ameobi bai taba bugawa Najeriya kwallo ba

Kocin Super Eagles Samson Siasia ya tabbatar da cewa dan kwallon Newcastle United Shola Ameobi zai bugawa Najeriya kwallo a karon farko a wasan sada zumunci tsakaninta da Guatemala.

Rahotanni daga kafafen yada labarai a Najeriya na cewar kocin Newcastle Alan Pardew ya bayyanawa Ameobi cewar kada yazo Najeriya saboda raunin da Andy Caroll ke fama da shi.

Sai dai Siasia ya tabbatar da cewar a ranar tara ga watan Fabarairu Ameobi zai takawa Najeriya leda.

Siasia yace"muna musayar wasika dashi, kuma ya tabbatar min cewar zamu hadu a Amurka inda za a buga wasan."

Kocin ya kara da cewar wasan da Guatemala zai taimaka wajen karawa kasar shiri a wasan share fage na neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika tsakanin Najeriya da Ethiopia a watan Maris.