Golan United Van der Sar zai yi ritaya a watan Mayu

van der sar
Image caption Edwin Van Der Sar ya koma United ne a 2005

Golan Manchester United Edwin van der Sar zai yi ritaya daga kwallo a karshen kakar wasa ta bana.

Dan kwallon Holland din mai shekaru arba'in da haihuwa ya koma Old Trafford ne daga Fulham a shekara ta 2005.

Van der Sar ya buga wasa tare da Red Devils sau 245 inda ya taimaka mata ta lashe gasar premier sau uku da kuma gasar zakarun Turai a shekara ta 2008.

Dan Holland din yace "lokaci yayi in maida hankali wajen iyalai na".

Tun a shekara ta 2009 ne Van der Sar ya fara kokwanto akan batun barin kwallo sakamakon rashin lafiyar matarshi Annemarie.

Nasarorin da VAN DER SAR ya samu:

*AJAX Eredivisie (1993/94, 1994/95, 1995/96, 1997/98) KNVB Cup (1992/93, 1997/98, 1998/99) Champions League (1994/95) Uefa Cup (1991/92) Uefa Super Cup (1995) Intercontinental Cup (1995) *JUVENTUS Uefa Intertoto Cup (1999) *FULHAM Uefa Intertoto Cup (2002) *MANCHESTER UNITED Premier League (2006/07, 2007/08, 2008/09) League Cup (2005/06) Champions League (2007/08) Fifa World Club Cup (2008)