Tennis:Novak Djokovic ya casa Andy Murray

djokovic Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Novak Djokovic

Dan kasar Serbia Novak Djokovic ya lashe gasar Australian open na tennis bayan ya samu galaba akan dan Birtaniya Andy Murray da seti biyu a jere.

Djokovic ya nunawa Murray ruwa ba tsaran kwando bane saboda an tashi 6-4, 6-2, 6-3.

Wannan ne karo na biyu da Djokovic ya lashe gasar Australian open a yayinda shi kuma Murray wannan ne karo na hudu da ake dokeshi a wasan karshe na babbar gasa a tennis.

Murray na kokarin kasancewa dan Birtaniya na farko cikin shekaru saba'in da biyar da zai lashe babban kofi na tennis wato Grand Slam.

A bangaren mata kuwa, 'yar Belgium Kim Clijsters ta lashe gasar bayan ta doke 'yar China Li Na a wasan karshe.