Sunderland ta sayi Muntari daga Inter Milan

sulley
Image caption Muntari bai ji dadin Inter ba lokacin Benitez

Sunderland ta kulla yarjejeniyar wucin gadi da dan kwallon Inter Milan Sulley Muntari daga nan zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Muntari me shekaru 26 ya taka leda a Portsmouth kafin ya koma Inter.

Dan kwallon Ghanan ya lashe kofina uku a bara tare da Inter Milan wato na Serie A da Coppa Italia da na zakarun Turai karkashin jagorancin Jose Mourinho.

Tun zuwan Rafael Benitez aka daina saka shi wasa sannan bata canza zani ba a lokacin sabon kocinsu a San siro wato Leonardo.

Muntari ya hade da 'yan uwanshi 'yan Ghana Asamoah Gyan da John Mensah a Sunderland.

Muntari ba zai buga wasansu na Talata ba tsakaninsu da Chelsea,amma ana saran zai shiga wasansu da Stoke City ranar Asabar mai zuwa.