Kofin FA:Obinna Nsofor yaci kwallaye uku

nsofor
Image caption Obinna Nsofor

Dan Najeriya Victor Obinna Nsofor ya zira kwallaye uku shi kadai inda ya taimakawa kungiyarshi West Ham tsallakewa zuwa zagaye na biyar na gasar cin kofin FA tsakaninsu da Nottingham Forest.

Obinna ya zira kwallon farko a minti hudu da fara wasan , kafin a tafi hutun rabin lokaci ya kara daya sannan yaci na uku bayan an dawo hutun rabin lokaci a bugun penariti.

Sakamakon sauran karawar zagayu na hudu na gasar kofin FA:

*Everton 1 - 1 Chelsea *Swansea City 1 - 2 Leyton Orient *Aston Villa 3 - 1 Blackburn Rovers *Watford 0 - 1 Brighton *Bolton Wanderers 0 - 0 Wigan Athletic *Burnley 3 - 1 Burton Albion *Birmingham City 3 - 2 Coventry City *Stevenage 1 - 2 Reading *Sheffield Wedn… 4 - 1 Hereford United *Torquay United 0 - 1 Crawley Town *Southampton 1 - 2 Manchester United *Arsenal 2 - 1 Huddersfield Town *Wolverhampton … 0 - 1 Stoke City *Notts County 1 - 1 Manchester City *West Ham United 3 - 2 Nottingham Forest