Liverpool za ta sayarda Torres akan pan miliyan 50

torres
Image caption Fernando Torres

Liverpool ta amince ta sayarda dan kwallonta Fernando Torres kafin karshen watan Junairu idan har Chelsea zata bada pan miliyan hamsin.

Tuni Liverpool tayo fatali da tayin pan miliyan talatin da biyar daga Chelsea akan dan kwallon Spain din mai shekaru ashirin da shida.

Torres ya koma Liverpool ne daga Athletico Madrid akan pan miliyan ashirin a shekara ta 2007.

Wani zabin da Chelsea keda shi shine ta bada pan miliyan arba'in ta hada da Nicolas Anelka.

A watanni masu zuwa ana ganin cewar Arsenal da Manchester United da Manchester City zasu fuskanci matsala akan 'yan kwallonsu Cesc Fabregas, Wayne Rooney da Carlos Tevez.