2014:Afrika ta Kudu ta mikawa Fifa kokon bara

jordaan
Image caption Jordaan ne ya shirya gasar kwallon duniya a 2010

Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika ta Kudu Danny Jordaan ya ce kasar za ta nemi daukar bakuncin gasar cin kofin zakarun nahoyiyin duniya a shekara ta 2014.

Jordaan ya bayyana haka ne lokacin da aka baiwa Afrika ta Kudu damar ta shirya gasar cin kofin kwallon Afrika na shekara ta 2017.

Ya ce akwai mahimmanci sosai Afrika ta dinga daukar bakuncin manyan gasar kamar gasar zakarun nahiyoyin duniya wato gasar da ake fafatawa tsakanin manyan kulob a duniya.

Jordaan ya shaidawa BBC cewar "zamu cigaba da tattaunawa da Fifa akan 2014".

Jordaan ne ya jagoranci shirya gasar cin kofin duniya na 2010 a Afrika ta Kudu, gasar da duniya tace an gamsar da ita.

Ya kara da cewar shirye shiryensu ya kankama wajen kaiwa Fifa bukatar kasar.

A taron da hukumar kwallon Afrika Caf ta gudanar a karshen mako a birnin Lubumbashi a Congo, an baiwa Morocco damar daukar bakuncin gasar Afrika na 2015 sannan Afrika ta Kudu ta dauki nauyin na 2017.