Dan Arsenal Nasri zai shafe makwani uku yana jinya

nasri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samir Nasri

Dan kwallon Arsenal Samir Nasri zai shafe makwani uku yana jinya sakamakon raunin daya samu a kafadarshi wasansu da Huddersfield.

Nasri mai shekaru ashirin da uku ya jimu ne bayan karon da yayi da golansu Manuel Almunia.

Akan haka akwai shakkun dan wasan ba zai buga wasan Arsenal da Barcelona na gasar zakarun Turai a ranar goma sha shiga ga watan Fabarairu.

Kocin Arsenal Arsene Wenger yace"Akwai alamun raunin Nasri mai tsananine".

Dan kwallon Faransa din na daga cikin manyan 'yan wasan Arsenal da suka taimaka mata kaiwa zagayen karshe na gasar cin kofin Carling.

Idan har tsohon dan kwallon Marseille din ya shafe makwanni uku yana jinya tabbas ba zai buga wasannin gasar premier tsakaninsu da Everton da Newcastle da kuma Wolverhampton.