An tilas ta mani komawa Liverpool-Carroll

carroll Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Carroll shine dan Ingilan da yafi tsada a kwallo

Dan kwallon Ingila Andy Carroll wanda ya koma Liverpool akan pan miliyan talatin da biyar, ya ce an tilastamashi barin Newcastle ne.

Dan kwallon ya shaidawa jaridar Evening Chronicle cewar"ban so na tafi ba,ya kamata in bayyanawa magoya bayanmu don su sani".

Kocin Newcastle Alan Pardew ya amince shine ya bukaci Carroll mai shekaru ashirin da biyu ya bada takarda neman izinin barin kulob din.

Pardew ya gayama jaridar Shields Gazette cewar: "na tattauna dashi akan batun sabunta yarjejeniya da bukatar ya sauya sheka".

A watan Disamba,Pardew ya bayyana cewar ba zasu sayarda Carroll ba saboda dan kwallon ya sabunta yarjejeniyarshi a watan Oktoba.

Haka zalika Newcastle da farko tayi fatali da bukatar sayarda Caroll, amma bayan da aka kara kudi sai kungiyar ta amince ta cefanar da dan kwallon Ingilan.