Man United ta doke Aston Villa da ci 3-1

Man United ta doke Aston Villa da ci 3-1 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wadannan kwallaye da Rooney ya zira za su rage sukar da ake yi masa

Wayne Rooney ya zira kwallaye biyu inda ya taimaka wa Man United ta doke Aston Villa da ci 3-1, abinda yasa ta kare jagorancinta na maki biyar a saman tebur.

Rooney ya fara zira kwallon farko ne kusan a minti daya da fara wasan.

Sannan ya kara ta biyu ana gab da tafiya hutun rabin lokaci, bayan da Nani ya tallafa masa.

Kwallon da Darren Bent ya zira ta bai wa Villa kwarin guiwa, amma sai dai kwallon da Nemanja Vidic ya zira ta kawo karshen fatan na su.

A yanzu dai Unitesd ta shafe wasanni 29 a gasar Premier ba tare da anyi nasara a kanta ba.

Sauran wasannin da aka buga

Arsenal 2-1 Everton Sunderland 2-4 Chelsea West Brom 2-2 Wigan