An nada Ammar Souayah a matsayin kocin Tunisia

benzarti Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Ben Ali ne ya 'matsawa' Benzarti

An sake nada Ammar Souayah a matsayin kocin kasar Tunisia a karo na biyu bayan Faouzi Benzarti ya sauka wata guda bayan da aka nadashi.

A watan Junairu ne Benzarti ya karbi mukamin a karo na biyu cikin shekara guda.

Amma sai ya sauka bayan zanga zangar da akayi a kasar wanda ya kawo karshen mulkin Zine al-Abidine Ben Ali.

A tattaunawar da yayi da gidan rediyon Faransa,Benzarti ya ce shugaba Ben Ali ne ya matsa mashi ya karbi mukamin.

Yace"fadar shugaban kasa ta bani kwarin gwiwa akan aikin".

Ammar Souayah ya karbi mukamin a lokaci mai tsauri saboda kalubalen dake gabanshi shine ya tsallakar da kasar ta buga gasar cin kofin kasashen Afrika a badi, kuma maki hudu kawai suka samu cikin wasanni uku