Chelsea za ta iya kalubalantar Man United-Rooney

rooney Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rooney ya zira kwallaye biyu a ragar Aston Villa

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney ya ce Chelsea zata iya yiwa kulob dinsu matsin lamba a yinkurin lashe gasar premier.

United ta dara Chelsea da maki goma akan teburin gasar, amma dai Blues din sun samu nasara a wasanninsu uku da suka wuce sannan kuma sun kashe pan miliyan saba'in akan siyo Fernando Torres da David Luiz.

Rooney yace"ba za a iya cewa lokaci ya kurewa Chelsea, saboda ba kanwan lasa bace".

Ya kara da cewar "amma mun san cewar mune zamu tuna yadda gasar zata karke, ina saran zamu daga kofin".

Chelsea wacce ke kokarin kare kofin data lashe a bara, kawo yanzu an doke ta a wasanni shida.

Amma ga alamu a yanzu Chelsea ta sha kwana saboda nasarar data samu akan Blackburn da Bolton da Sunderland,kuma watakila akwai sauran rina a kaba.