Adebayor na murnar cin kwallo a Santiago Bernabeu

adebayor Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Adebayor ya ji dadin barin Man City

Dan Togo Emmanuel Adebayor yace yayi murna matuka saboda zira kwallo da yayi a wasan da Real Madrid ta casa Sevilla daci biyu da nema a zagayen kusada karshe na cin kofin Copa del Roy.

Dan kwallon mai shekaru 26, ya je Real ne daga Manchester City a matsayin aro, inda ya shigo ana sauran minti goma a tashi wasan,sannan yaci kwallon.

Real Madrid kenan zata kara da babbar abokiyar hammayarta Barcelona a wasan karshe a ranar 20 ga watan Afrilu.

Adebayor yace "wasa ne na musamman a gare ni saboda ranar dana fara shiga fili naci kwallo a Santiago Bernabeu".

Tsohon kaptin din Togon sai da ya ajiye kwallon a kirjinshi bayan da Lassana Diarra ya bugo mashi sannan ya zira kwallon a raga.

Ita kuwa Barcelona ta tsallake zuwa wasan karshen ne bayan da suka lallasa Almeria daci takwas da nema a bugu biyu da suka yi karkashin jagorancin Pep Guardiola.

A shekarar 1990, Real ta hadu da Barcelona a wasan karshe inda Barca ta doke Real daci biyu da nema.