Ku daina kwatantani da Torres,in ji Carroll

carroll
Image caption Andy Carroll

Sabon dan kwallon Liverpool Andy Carroll yace baya fuskantar matsin lamba akan maye gurbin Fernando Torres a Anfeild.

Magoya bayan Liverpool suna nuna matukar goyon baya akan Torres kafin ya koma Chelsea a ranar Litinin akan pan miliyan hamsin.

An siyo Carroll daga Newcastle akan pan miliyan talatin da biyar jim kadan bayan tafiyar Torres, amma dan kwallon mai shekaru ashirin da biyu ya ce zai maida hankali wajen yin abinda ya kawo shi Anfeild.

Carroll yace"Torres goggen dan kwallo ne amma ina bukatar in maida hankali a nawa wasa, don in nuna irin tawa bajintar".

Carroll ya kasance dan kwallon da yafi kowanne tsada a tarihin Birtaniya sakamakon sauya sheka daga St James' Park to Anfield.