Saurez ya zura kwallo a wasan shi na farko a Liverpool

Sabon dan wasan da kungiyar Liverpool ta siya Luis Suarez ya zura kwallo a wasan shi na farko a Liverpool inda kungiyar ta doke Stoke City da ci biyu da nema.

Raul Meireles ne ya zura kwallon farko a wasan bayan an buga minti 47 a wasan.

Sannan kuma Saurez wanda aka sanyo wasan daga baya ya zura kwallo ne bayan minti 16 da shigo warsa fili.

Wannan ne dai wasan farko da Liverpool ta buga tun bayan ficewar Fernando Torres daga kungiyar inda ya koma Chelsea.