Barcelona ta kafa sabon tarihi a La Liga

messi
Image caption Lionel Messi yaci kwallaye 24 a gasar La Liga ta bana

Dan Argentina Lionel Messi ya zira kwallaye uku a wasan da Barcelona ta casa Atletico Madrid, inda kulob din ya kafa sabon tarihi na samun nasara a wasanni 16 a jere a gasar La Liga.

Nasarar tasa Barca kauda tarihin da Real Madrid ta kafa tun a shekarar 1960-1961 na samun nasara a wasanni 15 a jere.

Kocin Barca Pep Guardiola ya jinjinawa Lionel Messi inda yace bai san yadda Barcelona zata kasance ba tare da Messi ba.

Sakamakon sauran wasanni gasar La Liga:

*Athletic Bilbao 3 - 0 Sporting Gijón *Real Zaragoza 1 - 1 Racing Santander *Getafe 4 - 1 Deportivo *Almería 3 - 2 Espanyol *Osasuna 1 - 1 Mallorca *Villarreal 0 - 1 Levante