FIFA:Amos Adamu zai kara daukaka kara

amos
Image caption Fifa ta dakatar da Amos Adamu da Reynald Temarii

Tsohon wakili a kwamitin gudanarwar Fifa Amos Adamu ya ce zai daukaka kara zuwa kotun sauraron kararrakin wasanni wato CAS don cigaba kalubantar dakatarwar shekaru uku da aka yi mashi.

Bayan shafe kwanaki yana tattaunawa, kwamitin da Fifa ta kafa ya amince da hukuncin kwamitin da'a akan batun dakatar da Amos Adamu da kuma Reynald Temarii bisa zargin cin hanci wajen bada kuri'a akan kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 da 2022.

Amos Adamu yace"a tunani na kwamitin Fifa zai wanke ni, amma kuma abin takaici kwamitin bai yi hakan ba".

Ya kara da cewar"zan cigaba da daukaka kara akan batun har sai gaskiya tayi halinta.

A halin yanzu Amos Adamu ba zai shiga takarar neman kujara a hukumar kwallon Afrika wato Caf a yayinda Najeriya ta mika sunan Ibrahim Galadima don ya wakilci kasar a kwamitin.

A ranar 23 ga wannan watan ne za a gudanar da taron majalisar hukumar kwallon Afrika wato Caf a birnin Khartoum na Sudan inda za a zabi mambobi biyu daga cikin 24 da zasu wakilci nahiyar a Fifa.