Ancelotti ya kare Fernando Torres

Ancelotti ya kare Fernando Torres Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A karshen watan Janairu ne Torres ya koma Chelsea daga Liverpool

Kociyan Chelsea Carlo Ancelotti ya kare rawar da dan wasan da ya fi kowanne tsada a Burtaniya, Fernando Torres ya taka a wasansa na farko.

Torres wanda ya buya a wasan da Chelsea ta sha kashi a hannun Liverpool da ci daya mai ban haushi. A karshen watan da ya gabata ne ya koma Chelsea daga Liverpool.

"Na cire shi a minti na 60, abune mai kyau a gare shi ya fita daga wasan," a cewar Ancelotti.

Fernando gogaggen dan wasa ne, yana da kwarin guiwa, kuma bai nuna wata matsala ba kafin wasan."

Ya kara da cewa dole ne mu bashi lokaci domin ya fahimci tsarin wasanmu, kuma ina ganin zai yi hakan nan ba da jima wa ba.

Karin bayani