Gerrard ba zai buga wasan Ingila tsakaninta da Denmark ba

gerarrd
Image caption Steven Gerrard

Akwai alamun Steven Gerrard ba zai buga wasan sada zumuncin da Ingila zata kara da Denmark a ranar Laraba saboda rauni.

Gerrard wanda ya hade da sauran tawagar 'yan kwallon da Fabio Capello ya gayyata don tafiya birnin Copenhagen, amma kocin Liverpool boss Kenny Dalglish ya ce baya tunanin kaptin dinshi zai buga.

Rashin Gerrard zai talistawa kocin Ingila Capello nada sabon kaptin saboda dan kwallon Manchester United Rio Ferdinand shima rauni zai hanashi buga wasan.

Saboda rashin Gerrard da Ferdinand,ana saran Capello zai zabi tsakanin Franck Lampard ko Wayne Rooney don ya jagoranci tawagar.