Real Madrid ta lallasa Sociedad da ci 4-1

Real Madrid ta lallasa Sociedad da ci 4-1
Image caption Real Madrid na fatan kawo karshen kaka-gidan da Barca ta yi a Spain

Real Madrid na ci gaba da kokarin kamo Barcelona a kokawar da kungiyoyin biyu ke yi ta lashe gasar La Liaga bayan da ta doke Real Sociedad da ci 4-1.

Dan wasan Brazil Kaka ne ya bude fagen inda ya zira kwallon farko wacce kuma ta bai wa Real din kwarin guiwa.

Cristiano Ranlado ya ci gaba da ruwan kwallayen da ya ke yi a kakar bana inda ya zira kwallaye biyu a wasan.

Kafin daga bisani Emmanuel Adebayor ya kammala ruwan kwallayen, bayan da ya zira kwallonsa ta biyu a wasa biyun da ya buga kawo yanzu.

A yanzu Real Madrid na bin bayan Barcelona da maki bakwai a kan teburin na La Liga.