Kungiyar Wolfsburg ta Jamus ta kori Steve McClaren

mccaren Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption McClaren ne dan Ingila na farko daya zama koci a Jamus

Kungiyar Wolfsburg ta Jamus ta kori tsohon kocin Ingila Steve McClaren daga mukamin mai horadda 'yan kwallonta.

McClaren ya koma Wolfsburg ne bayan ya jagoranci kungiyar FC Twente ta lashe gasar kwallon kasar Holland.

Amma tun zuwanshi Wolfsburg ya kasa taka rawar da aka zata inda kungiyar ke matakin na goma sha biyu akan tebur kuma maki guda tsakaninta da wadanda zasu nitse.

Sanarwar da Wolfsburg ta fitar ta ce "Mun sallami Steve McClaren daga mukaminshi kuma Pierre Littbarski zai maye gurbinshi".

McLaren ya soma aikin mai horadda 'yan kwallo a kulob din Middlesbrough kafin yaja ragamar tawagar 'yan kwallon Ingila.

A lokacin da yake jagorancin Ingila, kasar bata tsallake zuwa gasar cin kofin kasashen Turai a shekara ta 2008 abinda ya sa aka koreshi a watan Nuwamban 2007.