An baiwa Rafael Nadal kyautar gwarzon dan wasanni na duniya

nadal
Image caption Rafael Nadal

An baiwa zakaran wasan tennis na duniya Rafael Nadal kyautar gwarzon dan wasanni na duniya a yayinda aka baiwa Lindsey Vonn 'yar tseren gudu a kankara irin wannan kyautar a bangaren mata.

A ranar Litinnin a birnin Abu Dhabi aka bada kyautukan a bukin bada kyautukan wasanni na Laureus.

Tawagar kwallon Spain data lashe gasar cin kofin duniya ce aka baiwa kyautar tim mafi bajinta a duniya a bara sai kuma shahararren dan tseren babur Valentino Rossi ya samu kyautar wanda yafi kowanne dan wasa ba zata.

Shi kuwa tsohon gwarzon dan kwallon duniya Zinedine Zidane na Faransa ya samu kyauta ce ta masamman a yayinda 'yar Amurka Kelly Slater ta samu kyautar 'yar wasa mafi bajinta a bara.

Shahararrun 'yan wasa 46 ne suke zabe a bukin kyautar Laureus.